Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Wani Matashi Mai Shekaru 17 Ya Dabawa Wani Mutum Almakashi Har Lahira a Zaria

0 565

Wani matashi mai shekaru 17 ya shiga hannun ‘yan sanda bayan da ya caccakawa wani mai shekaru 25 almakashi har lahira.

Lamarin ya faru ne a yankin Tudun wada da ke Zaria a jahar Kaduna bayan wani dan karamin rikici da ya barke tsakanin su.

Wani ganau, Abubakar Usman da ya yada labarin a shafin sa na Facebook ya bayyana cewa ba su ankara ba lokacin da fadan ya zama gagarumi.

Ya ce kwatsam suka ga matashin ya fito da almakashi ya dabawa mutumin a kafadar shi da kirjin shi, lamarin da ya haddasa rasuwar shi.

Usman ya yi amfani da wannan abu wajen yi wa mutane tuni da koyarwar Manzan Allah (S.A.W) na kai zuciyar mu nesa, musamman idan muka yi fushi.

A cewar shi ” Duk wanda ya bijirewa koyarwar manzan Allah zai yi da na sani duniya da lahira.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...