Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Wata Inyamura Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ta Karbi Addinin Musulunci

0 471

Wata Inyamura da ta karbi addinin musulunci mai suna Aishat Obi ta bayyana cewa ta yi haka ne saboda kyan hali irin na wata aminiyarta musulma mai suna Faddylado Sama.

Aishat ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafin ta na Facebook dauke da hotouna ta na aminiyar ta ta, inda ta kira ta da ‘yan biyunta.

KARANTA WANNAN: Wasu mata 2 da yarinya daya sun karbi addinin musulunci a Bauchi

A cewar ta, “Wannan ita ce ‘yan biyu na da ta fito daga mahaifa daban. Ta wuce gaban ‘yar uwa a guri na kuma ta na daya daga cikin wadanda kyan halin su ya ja hankali na zuwa addinin musulunci. Ina roko Allah ya sa na samu kawa kamar ta a rayuwa ta ta gaba. Ina rokon Allah ya bani irin kyan halin da zai iya sauya wasu. Ina rokon Allah ya sani na yi rayuwa irin ta muminai mata”

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...