Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Yadda Za Ka Samma Masoyanka Mb Na Data Ta Layin 9Mobile (Etisalat)

0 674

9mobile ta baiwa masu amfani da layin ta damar samma masoyar su Mb kyauta ko kuma su siyar da Mb na su a duk lokacin da suka ga dama.

 

Idan kun dade kuna neman yadda ake samma mutane, ‘yan uwa da abokanen arziki data to ba sai kun je wani wuri ba, gashi nan a saukake. Samma Data a 9mobile wato 9mobile Data Share ya ba masu amfani da layin 9mobile damar raba Mb na su na waya ba tare da samun wani ciwon kai ba, ta hanya mai sauki. Abunda mutum kawai zai shine zai danna wasu lambobi ne kawai wadanda ake kira da suna USSD Code. Ga yadda ake raba Mb din a kasa:

Yadda Ake Samma Masoya Mb way

  • Yadda za ku iya samma masoyar ku data na waya a saukake, da farko da za a danna lambobin nan kamar haka *229*PIN*Yawan Mb Na Data Da Za Ka Aika*Lambar Wayan Wanda Za Ka Aikawa Data#

 Misali: *229*0000*20*090234567888#

–  Bayan an aika wannan lambar mutum zai samu sako daga cibiyar sadarwa na 9mobile inda za su ruwaito masa da cewa suna nan suna aiki akan abun.

–  Bayan an mintuna kadan za su sake aiko wani sakon daban kuma inda za su bayyana cewa ka turawa lambar masoyinka 50mb na data.

Bayanin Kulawa:

1. Ba za a iya tura Mb data fiye da 50mb ba, amma duk abunda yayi kasa da haka za a iya turawa ga masoya.

2. Sannan kuma ba za a iya tura fiye da data Mb fiye da 200mb a rana ba.

3. Idan mutum na so ya turawa masoyarsa data kamar na 200mb, sai ya tura code din 50mb so 4. idan aka 50 x 4 = 200,  wato idan aka hadda hamsin(50) so hudu(4) za a samu 200.

 

Yadda Ake Canza Lambobin Pin Din Raba Data

A farko dai kamar yadda ku ka sani, ko wace sim na zuwa da pin iri daya ce wadanda su ne ‘0000’, amma don tsaro mutum zai iya canza wadannan zuwa lambobin da ya ke so.

Yadda ake canza tsofin lambar pin din raba data wanda ke zuwa da sim zuwa ga lambar da ka ke so.

  • Don canza lambobin default pin na sim zuwa lambar da ku ke so, za ku danna *247*Tsohon Lambobi*Sabbin Lambobi#

Misali: *247*0000*1234#

Bayanin Kulawa: Ba dole bane sai mutum yayi amfani da lambobin da aka amfani da su a wurin yin misali ba, kowa zai iya kirkiro irin ta sa lambobi 4 da ya ke so.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...