Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

Yadda Za Ka Tsare Shafinka Na Facebook Daga Masu Kutse

0 877

Kutse a shafukan sada zamunta ya zama ruwan dare a baya-bayan nan ta yadda kawai sai dai mutum ya tashi ya ga ya yi sharhi akan batun wani bayan kuma a zahiri ya san bai yi ba. Ko kuma ya yi kalama batanci ga wani ko wasu, kai wani lokaci ma kaga mutum da mutuncinsa amma sai kaga ya ɗora hotunan batsa ko bidiyo na batsa ko dai wani abu na rashin mutunci

 

Sau tari za ka samu ba ma za ka san akwai wannan abu a shafinka ba, da sunanaka ba har sai wani ya nusar da kai. Wannan aikin masu kutse ne, kuma illarsu na da yawa cikin har da sarayarwa da mutum mutunci babu gyara babu dalili, tare da jefa mutum cikin hatsarin da ya shafi harkokin tsaro da dai sauransu

 

Ga hanyoyin da za ka bi don kaucewa mugun aikin masu kutse:

 

1. Yana da kyau ka dinga canja password din ka akalla bayan sati daya (1) zuwa sati biyu, sannan wajen canjawar a guji sanya 123456 ko sunanka, ko kuma lambar wayarka, sunan budurwarka, ko unguwarka, a’a yana da kyau ka sanya harufa da kuma lambobi, kai harma da symbols kamar @”-+, sannan kada ka yarda ka sanar da wani wannan password din naka.

Sannan a kula kada kayi amfani da password guda daya a dukkan abubuwanka misali a Email dinka da kuma facebook din ka da sauran abinda kake budewa duk su zama iri daya domin hakan zai baiwa wasu damar yin awon gaba da account dinka.

 

2. Sanya Karin email akan account dinka. Ina bada shawarar kayi adding email kamar guda uku (3) akan account dinka, wannan zai baka cikakken iko akan account dinka duk wani motsi ko wani yunkuri da aka yi kai tsaye za ka gani, sannan a setting na email din ka mayar dashi babu wanda zai iya ganin su sai kai kadai wato “only me” a yaren facebook.

 

3. Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki kana samun sakonni a cikin ta da yawan mu lambobin da muka bude facebook da su mun rasa layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar daga kan facebook din mu canza ta da lambar da muke da ita a yanzu, rashin yin hakan zai bamu matsala don haka idan kasan ka rasa layin ka to ka canza lambar layin ka na yanzu domin ka cigaba da samun sakonnin facebook.

 

4. Ka sanya “Login Approval” a account dinka, yadda zaka sanya shine ka bi wannan hanyar kaje :Home ,sai ka tafi,-> Account Settings,sai ka sake shiga -> Security,sai ka kuma shiga -> Login Notification sai ka mai da shi “Enable”. Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na account dinka sannan idan za ka yi login dole sai an turo maka da code ko kuma ka yi approving ta wayarka idan android ce, sannan anan bangaren zaka iya samar da “code generator” ta yadda zaka samar da wani code wanda kai kadai ne ka sanshi idan kazo yin login bayan password to shi ma zaka saka shi.

 

5. Sannan zaka iya zabar wasu amintattu daga friend dinka kamar Grantor kenan ka sanya su,
suma zasu iya baiwa account din ka kariya.

 

6. Ka samar da tsayayyiyar browser da kake hawa facebook, kada ka zama yau ka ari wayar wancan ka hau gobe ka ari ta wancan, sannan a daina yin saving din password a browser saboda zaka iya yadda wayar ka, ko kuma a dauke maka ita, musamman a wannan lokacin da ake yawan kwace kaga wani zai iya hawa, sannan facebook zasu iya yi maka blocking saboda yawan yin hakan.

 

7. Ka dinga yin log out duk sanda ka hau idan zaka sauka.

 

8. Kada ka baiwa wani ko wata bayanan ka na yin login a account din ka ko wani web site.

 

9. Kayi tunani kafin ka danna link, zaka ga ance ka danna link, to ka fara yin tunani kafin ka shiga,
misali ace ka danna kaga abinda zai faru ko makamantan hakan, ko idan ka shiga sai kaga ance ka saka password dinka to duk irin wannan sai a kiyaye.

 

10. Kayi login a www.facebook.com ko www.fb.com kada kayi login a facebook ta kan wani site daban ba wannan ba, ko application wanda ba ingantacce ba.

 

11. Ka dinga yin updating din browser din ka ko application din ka.

 

12. ka dina installing anti virus a wayar ka ko a computer da kake amfani da ita.

 

13. ka daina yawan tura Requesting ko yawan yin accepting ka kula wajen karbar wanda baka san shi ba, yana da kyau ka duba profile din sa kafin kayi accepting din sa.

 

14. Ka daina yawan yin sharing na wani link da baka tantance shi ba.

 

15. ka daina hade facebook account dinka da ko wane shafukan internet, zaka ga da yawa daga website ana yin register din su ta facebook mai makon kayi da email sai kayi da facebook
shima wannan ya kamata ayi tunani sosai kafin aiwatarwa.

 

16. Kada kayi wani posting wanda ya sabawa wadansu to idan suka yi ta yin reporting din sa ga facebook su ma za su yi blocking din account dinka.

 

Allah yasa mu dace, amin.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...