Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

‘Yan Bindiga Sun Boye Gawarwakin Wasu Yara 2 A Cikin Firijin

0 141

Wasu ‘yan bindiga sun kashe wasu yara 2 a ranar Laraba a garin Obiokpok da ke karkashin karamar hukumar Nsit Ibom a jihar Akwa Ibom.

 

Karanta wannan: Dan sanda Ya Kashe Dalibar Kwaleji Kan Cin Hancin N200

 

An samu labarin cewa yaran 2 da aka kashe, ‘yan bindigan sun saka gawarwakin sun a cikin firijin bayan mahaifin na su, Aniekan Billie, ya tafi kasuwar Kpokpo siyan kayan abinci.

 

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Sanatan Nijeriya, Sun Bukaci Kudin Fansa Miliyan N80

Fadin mahaifin na su, ya gano gawarwakin ‘ya’yan na sa 2, Godwin Sunday, (dan shekaru 9) da Idara Sunday, (‘yar shekaru 5) a cikin firijin bayan ya dawo gida.

 

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga Sun Kai Haren Ba Zata A Wani Kauye, Sun Kashe Mutane 2

 

Kakakin ‘yan sanda reshen jihar Akwa Ibom, Mr. Bala Elkana, ya tabbatar da faruwan haka ga manema labarai, inda ya ce an mika karar zuwa ofishin ‘yan sanda a misalin kare 2:55 na rana.

 

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga Sun Sace Wata Dalibar Jami’ar Jihar Kwara (KWASU)

 

“Wani mutum wanda ake kira da suna, Aniekan Sunday-Billie, daga Obiokpok da ke karkashin karamar hukumar Nsit Ibom ya zo ofihsin ‘yan sanda a ranar 5 ga watan Disamba, 2017, a misalin karfe 2:35 na rana don mika karar kisar ‘ya’yan sa 3 masu suna one Godwin Sunday, (dan shekaru 9); da Idara Sunday, (‘yar shekaru 5), da kuma  Godspwer Sunday, (dan watanni 7), bayan ya kulle su a cikin gida a unguwar Mbioporo 1 sannan ya tafi kasuwar Urua Kpokpo don siyan kayan abinci.

 

“Ya ce da dawowarsa gida, ya tsince gawarwakin ‘ya’yan sa 2, Godwin da Idara a cikin firjin na tebur,” ya ce.

 

Karanta wannan: ‘Yan Bindiga Sun Kai Mumunan Hari Bankin ‘First Bank’ Da ‘UBA’ a garin Lappai

Jami’in hulda da jama’a ya kara da cewa ‘yan sanda na gudunar da bincike game da lamarin don ganin cewa an cafke wadanda suka kashe yaran.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...