Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Tsohon Alkalin Alkalai Tare Da Kashe Wani Dansanda

0 109

Rahotanni sun bayyana cewa wasu yan bindiga sun kai farmaki gidan tsohon Alkalin Alkalai, Mahmud Muhammad dake unguwar rimi a garin Kaduna.

 

‘Yan bindigan sun kai farmaki gidan ne a ranar Laraba 10 ga watan Janairu da misalin karfe 8:30 na dare da niyyar hallaka Mahmud.

 

Isar su gidan ke da wuya, suka bude wuta ga jaruman Yansanda guda biyu, yayin da suke musayar wuta da ‘yan sandan ne daya daga cikin ‘yan sandan mai suna sajan Yakubu ya mutu nan take, inda aka kuma garzaya da dayan mai suna Abdullahi Adam asibiti.

 

Mahmud Muhammad dai shine tsohon Alkalin Alkalai, wanda ya sauka ya mika ma Alkalin Alkalai mai ci a yanzu, Walter Onnoghen.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...