Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

‘Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata ‘Yar Shekaru 38 a Birnin Abakaliki

'Yan Bindiga Sun Sace Wata Mata 'Yar Shekaru 38 a Birnin Abakaliki

0 145

‘Yan bindiga sun sace wata mata, Mrs Ijeoma Nweke, ‘yar shekaru 38 a unguwar Dr. Laz Nwuzor da ke yankin Hill Top a birnin Abakaliki.

 

An gano cewa matar da aka sace na hanyar zuwa ibadar a cocin St. John the Evangelist Catholic Church tare da ‘yar ta ‘yar shekaru 13 da  kuma wasu ‘yan uwanta.

 

 

‘Yan bindigan Mrs Nweke kawai suka sace a yayin da ita ‘yar na ta ta tsere daga hannunsu kafin ta kai kara zuwa wurin ‘yan sanda.

 

Jami’ar hulda da jama’a na rundunar yan sanda reshen jihar Ebonyi, Mrs Lovett Odah, ta tabbatarwa manema labarai da faruwan hakan a misalin karfe 5 na safiyar Asuba a ranar Litinin.

 

Karanta wannan: Sojoji Sun Kwato Mutane 46 Daga Hannun Boko Haram Bayan Sun Kakkabe Sansanin Sabil Huda

 

Ta ce ‘yan sanda suna nan suna gudunar da bincike a kan sace matar da ‘yan bindiga suka yi.

 

“Wasu maza wadanda ake zargi masu satan mutane ne  sun fito daga wani daji, suka bi Nweke har sai da suka samu nasaran sace ta a yayin da ta ke hanyar zuwa ibadar da safe a cocin St John the Evangelist Catholic Church.

 

“‘Yar matar da aka sace ta samu nasaran tserewa daga hannun ‘yan bindigan, daga nan ta dawo gida ta fadawa mahaifinta, Mr John Nweke, wanda shine ya kai rahoton sace matar da ‘yan bindigan suka yi ga ‘yan sanda.

 

Karanta wannan: Wani Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Nijeriya Zai Tsaya Takarar Shugaban Kasa a 2019

 

“Muna nan muna gudunar da bincike a kan lamarin don ceto ita wannan matar a cikin  koshin lafiya tunda ‘yan garkuwa ba su tuntubi iyalan matan ba don amsan kudin fansa.

 

“Rundunar ta aika jami’anta daga sashen yaki da fashi da makami da kuma garkuwa da mutane (SARS), wadanda ke iya kokarinsu wajen ganin cewa sun cafke wadanda ake zargi da aikata wannan mummunar aiki tare da ceto ita wannan matar,” Odah ta ce.

 

Karanta wannan: Sirikina Ne Ya Cancanta Ya Gaje Ni – Gwamna Okorocha

 

A karshe kuma ta bukaci al’ummar jihar da su kasance masu kulawa tare da kawo karar duk wani abunda suka gani a yankunan su wanda da su yarda da shi ba zuwa ga ofishin ‘yan sanda ko kuma hukumomin jami’an tsaro da ke kusa da su.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...