Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

‘Yan Fashi Sun Yashe Gidan Mista Ibu, Sun Yi Awan Gaba Da Miliyan 14.3

0 280

A ranar Asabar da ta gabata ne ‘yan fashi suka afka gidan shahararren jarumin barkwancin nan a masana’antar Nollywood, John Okafor wanda aka fi sani da Mista Ibu, inda suka yi awan gaba da kudade da kayyaki na miliyoyin Nairori.

A rahotan da Mista Ibu ya kai ofishin ‘yan sandan jahar Lagos, ya ce kudaden da aka sace masa sun kai miliyan 14.3

 

Ya ce a lokacin da abun ya faru, matar shi kadai ke gida, yayin da shi ya yi tafiya.

KARANTA WANNAN: ‘Ya sanda sun kashe wasu ‘yan fashi da makami 3

Ya ce matar ta fada masa yadda ‘yan fashin suka fara ta’asar da misalin karfe 3:00 na dare har sai da suka kai misalin karfe 4:25 na suba kafin su tafi da kayyaki da kudaden da suka sata.

 

Mista Ibu dai ya na daga cikin manyan jaruman barkwanci a Nijeriya baki daya.

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...