Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

‘Yan Kunar Bakin Wake 3 Sun Kashe Kansu a Kofar Asibiti a Maiduguri

0 305

‘Yan kunar bakin wake uku dukkansu mata sun tada boma boman da ke jikin su a kofar baya ta asibitin da ke yankin Molai a Maiduguri babban birnin jahar Borno.

Sai kuma wani dan kunar bakin wake namiji da shi ma ya tada na shi bom din a wani jejin da ke kusa da asibitin.

Banda ‘yan kunar bakin wake, babu wanda ya samu ko kwarzane.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jahar Victor Isuku shi ya bayyana haka wata sanarwa da ya aikawa manema labarai.

Ya ce lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar da ta gabata.

Sai dai Isuku ya ce akwai yiwuwar wasu daga cikin ‘yan kunar bakin waken sun bazama cikin gari, a don haka ne ya yi kira da mazauna yankin da su sanya ido su kuma kai rahoto wajen ‘yan sanda da zaran sun ga wani abu da ba shi kenan ba.

 

 

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...