Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

‘Yar Gidan Aliko Dangote, Fatima Na Shirin Amarcewa

0 814

Masu hasashe dai na da ra’ayin wannan biki shi zai kasance bikin da ya fi kowanne kayatarwa a tarihin Nijeriya.

‘Ya ga attajirin dan kasuwa kuma mutumin da ya fi dukiya a Nahiyar Afrika, Alhaji Aliki Dangote mai suna Fatima za ta auri da ga tsohon insfeka janar na ‘yan sanda, MD Abubakar mai suna Jamil.

KARANTA WANNAN: Dangote ya kara rike kambun attajirin da ya fi arziki a Afrika

Za a daura auren ne a watan gobe na Maris a Eko Hotel da ke jahar Lagos.

Bikin dai zai samu halartar masu fada a ji daga ko’ina a duniya, a ciki har da daya daga cikin wadanda suka fi kudi a duniya; Bill Gates.

Rahotanni sun bayyana cewa kimanin shuwagabannin kasa 5 ne za su halarci bikin, haka zalika an gayyaci gaba daya tsoffin shuwagabbannin Nijeriya.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...