Samu labatai da duminsu, tsugungumi, gulma, labarin finafinai da taurari, mawaka, makada da wakoki, zamantakewa, hirarraki da sauran abubuwa na musamman. Karanta abubuwan da muka zo maka da su yau!

An Yi Gaggarumin Zanga Zangar Yaki Da Al’adar Yi Wa Mata Kaciya A Abuja

An Yi Gaggarumin Zanga Zangar Yaki Da Yi Wa Mata Kaciya A Abuja

0 237

Rahotanni sun bayyana cewa masana, kwararru tare ‘yan raji da shugabannin al’umma sun gudanar da wani gangamin zanga zangar yaki da al’adar yi wa mata kaciya a Abuja, musamman a ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin fadakarwa kan wannan mummunar dabi’a.

 

An gudanar da wannan zanga zangar ne musamman domin fadakar da ungozoma irin matakan da zasu dauka na gano mai fama da wani ciwo dake da alaka da irin wannan kaciya ta mata domin garzayawa da su asibiti maimakon barinsu su haihu a gida a lokacin nakuda.

 

Ms Comfort Mahdi, Wata jami’a mai kula da daidaito a tsakanin jinsuna ta ce mata da yawa da aka yi ma kaciya ba su iya sakewa da miji ko da a gidajensu na aure, abinda ke janyo matsalar zamantakewa, yayin da wasu da yawa daga cikinsu ke fuskantar wahala a lokutan haihuwa.

 

KARANTA: Za A Hukunta Duk Wanda Aka Kama Da Yiwa Yara Mata Kaciya A Jihar Ekiti

 

Ta ce wannan al’ada da ake yi a wasu sassa da nufin hana mata bin maza, babu abinda take haifarwa illa wahala har ma da mutuwa.

 

Wani Dakta mai suna Rilwan Mohammed yace a saboda ganin yadda ake samun karuwar mata masu fama da illolin da suka jibinci kaciyar da aka yi musu, ya sa tilas a gudanar da irin wannan fadakarwa a yankunan karkara, inda aka fi yin wannan abu.

 

DUBA: Wanzami Ya Illata Wata Amarya Da Sunan Kaciya A Kano

 

Shi kuma Dakta Usman Sa’idu Adamu, yace su na tura jami’ai domin kula da duk wadda aka samu labarin tana fama da wannan matsala.

Comments
Loading...
Dakacemu....

Shiga tsarin samun sakonninmu.

Shin kana son ka ke samun haske akan dukkan abubuwan da ke wakana a shafin Alummata? Shigar da adireshin email dinka da sunanka a nan kasa, za ka yi farin ciki ka aikata hakan...